Home Labaru Rikicin Magoya Baya: INEC Ta Yi Barazanar Dakatar Da Zabukan Edo Da...

Rikicin Magoya Baya: INEC Ta Yi Barazanar Dakatar Da Zabukan Edo Da Ondo

327
0
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta yi barazanar dakatar da shirye-shiryen gudanar da zabukan gwamnoni da za a yi a jihohin Edo da Ondo, idan har abubuwan da ‘yan siyasa ke aikatawa ya jawo tarzoma da karya doka.

Kwamishina na Kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe a hukumar, Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a nan Abuja bayan wani taro tsakanin hukumar da masu ruwa da tsaki a zabubbukan, inda aka tattauna kan al’amura da dama, ciki har da shirye-shiryen zabubbukan.

Okoye, ya ce, hukumar tana cikin damuwa matuka da yadda al’amura ke kara rincabewa wajen abubuwan da jam’iyyun siyasa, da ‘yan takara da magoya bayan su ke aikatawa tare da furta maganganun tada fitina a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zabubbukan.

Ya ce wadannan abubuwan sun hada har da lalata kayan kamfen na abokan adawa kamar su allunan talla tare da yakar juna ta hanyar rikici da furta muggan kalamai.

Ya ce yana da muhimmanci jam’iyyun siyasa, da ‘yan takara da magoya bayan su su san cewa akwai dokoki da ka’idoji da aka shimfida wadanda wajibi ne a bi su a lokacin yakin neman zabe dan haka hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyan ta na tabbatar da an bi doka da oda.

Leave a Reply