Home Labaru Almundahana: An Zargi Tsohuwar Gwamnatin Bauchi A Lakume Naira Biliyan 2.3 A...

Almundahana: An Zargi Tsohuwar Gwamnatin Bauchi A Lakume Naira Biliyan 2.3 A Kan Jana’iza

290
0

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce, tsohon Gwamnan jihar Mohammed Abubakar ya kashe Naira biliyan 2 da miliya 300 wajen saya wa mamata linkafani da wasu kayayyakin jana’iza a cikin watanni biyar kacal.

Mai magana da yawun Gwamna Dakta Ladan Salihu ya shaida wa manema labarai cewa, an kashe kudaden ne tsakanin watan Janairu zuwa Mayu an shekara ta 2019.

Dakta Salihu ya ce, an kashe sama da Naira miliyan 900 wajen sayen linkafanin mamatan, yayin da aka kashe Naira biliyan 1da miliyan 400 wajen sayen katakan da ake shinfidawa a cikin kaburbura.

Sai dai tsohon Gwamnan ya musanta zargin, wanda ya bayyana a matsayin abin dariya, amma gwamnati mai ci ta ce ta na da shaida a kan wannan lamari.

Leave a Reply