Home Labaru Takaddama: Masarautar Kano Ta Sha Alwashin Maka Hukumar Yaki Da Rashawa Kotu

Takaddama: Masarautar Kano Ta Sha Alwashin Maka Hukumar Yaki Da Rashawa Kotu

453
0

Majalisar masarautar jihar Kano ta sha alwashin shigar da kara A kan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano, bisa raina umurnin kotu.

A cikin wata wasika da aka aike wa shugaban hukumar, lauyan masarautar ya ce hukumar ta ki bin umurnin kotu ta hanyar gayyatar tsofaffin ‘yan masarautar domin gudanar da bincike.

Wasu daga cikin ‘yan masarautar da aka gayyata dai sun hada da Mukhtar Adnan, da Isa Hashim, da kuma Yusuf Bayero.

Har ila yau, hukumar ta aika da takardar gayyata zuwa ga matar Sarki Muhammadu Sanusi, da kuma matan tsohon sarkin Kano marigayi Ado Bayero guda biyu.

Hukumar dai ta yi zargin cewa, sama da mutane 30 ne su ka amfana daga naira biliya 3 da miliya 400 na kudin da aka yi almubazaranci da su a karkashin sarki Sanusi.

Lauyan Masarautar ya ce, kotun jihar da babbar kotun Tarayya da ke Kano, sun umurci hukumar ta dakatar da duk ayyukan da su ka shafi bincike a kan kudaden masarautar.

Leave a Reply