Home Labarai Alkawari Daya Ne Ba Mu Cika Wa Shekarau Ba — Kwankwaso

Alkawari Daya Ne Ba Mu Cika Wa Shekarau Ba — Kwankwaso

123
0

Dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce babu wata matsala tsakaninsa da Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau da har zai sa ya fice daga jam’iyyar.

Kwankwaso na tsokaci ne kan rahotannin rashin jituwar da take tsakanin tsoffin Gwamnonin na Kano biyu wanda har ake rade-radin Shekarau zai fice daga NNPP,Kwankwasoninda ya kara da cewar duk abin da ake fada ba gaskiya ba ne.

Ya kara da cewar lokacin da Shekarau da magoya bayansa suka shigo shigo jam’iyyar Babu sharadin da suka gindaya wa NNPP da ba a cika musu ba, illa batun ’yan takara wanda kuma jam’iyyar ta iya bakin kokarinta amma lokaci ne ya kure

Sannan sai ya ce, mutanen da duk Shekarau ya zo da su daga APC masu son yin takara, lokaci ya kure da INEC ba za ta karbe su ba.

Sai dai ya ce sun yi wa mutanen Shekarau alkawarin manyan mukamai  gwamnati idan jama’iyyarsu ta kafa gwamnati a 2023

Leave a Reply