Home Labarai Cocin Katolika Ta Karbi Tuban Gwamnan Filato

Cocin Katolika Ta Karbi Tuban Gwamnan Filato

85
0


Cocin Katolika da ke jihar Filato ta ce ta karbi ban hakurin da Gwamnan Jihar, Simon Lalong ya yi kan maganganun da ya yi lokacin da aka nada shi, Daraktan yakin neman zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC.

Archbishop na Cocin Katolika da ke Jos, babban birnin jihar Filato, Archbishop Rabaran Matthew Ishaya Audu je ya bayyana karbar yafiyar a madadin cocin.

Rahotanni sun nuna kalaman Gwamnan a kan takarar Musulmi biyu a jam’iyyar ba su yi wa cocin dadi ba.

Archbishop Matthew Ishaya Audu, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron cocin na kasa karo na 19, da aka gudanar a Cocin Louis Parish da ke Jos.

babban taron Bishop-Bishop na wannan Coci, karkashin jagorancin Shugabansu na cocin Katolika, ya amince tare da karbar wannan ban hakurin da gwamna Lalong ya yi

Ya kuma ce cocin na karfafa wa mabiyanta gwiwa kan su shiga harkokin siyasa.

Ya bai wa gwamnan tabbacin cewa cocin ba za ta ba shi kunya ko kuma ta bari ya fadi a wannan jagorancin d

Leave a Reply