Gamayyar kungiyoyin kwadago na Nijeriya, sun yi watsi da furucin ministan kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige, cewa gwamnatin tarayya na bukatar rage yawan ma’aiktan kafin ta samu damar kaddamar da mafi karancin albashin Naira 30,000.
Sakataren kungiyar Alade Lawal ya shaida wa manema labarai cewa, ko kadan wannan barazanar da gwamnati ke yi ba ta shiga jikin su ba.
Ya kuma yi korafi a kan maganar da Ngige ya yi cewa, gwamnati na bukatar kudin da yawan su ya kai Naira biliyan 580 duk shekara domin biyan ma’aikata mafi karancin albashin.
Lawal ya cigaba da cewa, duk wanda ke tunanin cewa za a rage yawan ma’aikata ta hanyar sallamar wasu ya na bata bakin sa ne kawai.
Ya
ce gaba daya yawan ma’aikatan Nijeriya bai kai miliyan daya ba, idan kuwa har
da gaske gwamnatin tarayya ke yi abu ne da bai fi karfin ta ba.
You must log in to post a comment.