Alƙalin babbar kotun tarayya da ke Abuja Mai Sharia James
Omotosho, ya ƙi sa hannu a kan takardar sakin jami’in ɗan
sanda DCP Abba Kyari duk da bada belin sa da ya yi a kan
Naira miliyan 50.
Mai Sharia Omotosho dai ya bada da belin DCP Abba Kyari, wanda ya shafe tsawon watanni 18 a kurkukun Kuje da ke Abuja bisa tuhumar rashin bayyana kadarar da ya mallaka.
Sai dai alƙalin ya ce ba zai sa hannu a sake shi ba har sai an bada belin sa a wasu shari’o’in da ya ke fuskanta, wadanda su ka danganci safarar miyagun ƙwayoyi.
Idan dai ba a manta ba, a ranar 23 ga watan Maris ne Mai Shari’a Emeka Nwite ya ƙi bada belin Abba Kyari a karo na biyu, game da zargin safarar miyagun ƙwayoyi da ake yi masa tare da wasu jami’an ‘yan sanda.














































