Home Labarai Akwa Ibom: Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Kan Satar Yara 5

Akwa Ibom: Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Kan Satar Yara 5

237
0
Nigeria Police Force (1)
Nigeria Police Force (1)

Rundunar ‘yansanda ta jihar Akwa Ibom ta kama wani mutum bisa zargin satar wasu yara biyar ‘yan gida ɗaya.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, Joseph Eribo ne ya bayyana haka, jiya Litinin, a lokacin gabatar da wanda ake zargi mai suna Promise Boniface, tare da wasu tarin waɗanda ake zargi da aikata miyagun laifuka da aka kama.

An kama mutumin ne wanda ake zargin ya sato yaran daga wani gida a ƙaramar hukumar Obio Ibiono, bayan da haɗakar ‘yan sanda da mutanen ƙauyen suka yi farautarsa.

‘Yansanda sun ce da ana bincikensa Boniface ya ce ya samu yaran ne suna gararamba sun rasa na yi a cikin ruwan sama sai ya ɗauke su.

 Da aka matsa da bincikensa sai ya yarda cewa sato su ya yi, amma ya ce yanayin yunwa ne ya sa shi haka, kuma wannan shi ne karon farko da ya taɓa yi.

Kwamishinan ‘yansandan ya ce tuni an damƙa yaran ga iyayensu cikin ƙoshin lafiya, kuma bayana kammala bincike za a gurfanar da mutumin d ake zargi da satar a gaban kotu.

Sabon ƙudurin haraji ba zai soke wasu hukumomi ko talauta Arewa ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Leave a Reply