Jagoran sashen kula da kiwon lafiya na hukumar alhazai ta Nijeriya Ibrahim Kana, ya ce adadin yawan alhazan Nijeriya da su ka rasu a kasar Saudiyya ya kai akalla mutane Tara.
Ibrahim Kana ya bayyana haka ne, yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai a Mina, inda ya ce daga cikin mutanen da su ka rasu akwai wata mata daga jihar Legas.
Karanta Labaru Masu Alaka: NAHCON Ta Karrama Limamin Daya Ceci Kiristoci 300
Ya ce matar ta rasu ne bayan an kai ta asibitin Mina, sannan a lokacin ne su ka gane cewa hawan jinin ta ne ya tashi farat-daya.
Shugaban
tawagar mahajjatan jihar Lagos Abdulateef Abdulkarim, ya ce sunan matar
Folashade Lawal daga karamar hukumar Oshodi, kuma ta rasu ne da misalin karfe
uku na Asuba a wajen jifar shaidan.