Home Labaru Aisha Buhari Ta Roƙi A Kawo Karshen Yaƙin Sudan

Aisha Buhari Ta Roƙi A Kawo Karshen Yaƙin Sudan

343
0

Uwar gidan shugaban kasa A’isha Buhari, ta roƙi a haɗa karfi
da karfe domin ganin kurar rikicin Sudan ta kwanta.

A’isha Buhari ta yi kiran ne, a wani taro da ta jagoran ta a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ta ce akwai rawar da matan shugabannin Afirka za su iya takawa musamman wajen kai agaji a kasar Sudan.

Tun ranar 15 ga watan Afrilu ne yaƙi ya ɓarke a Sudan, kuma an kasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin.

Sama da mutane 500 ake kyautata zaton cewa rikicin ya yi sanadiyyar rasuwarsu ya zuwa yanzu.

Leave a Reply