
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutters, ya ce sun kafa kwamitin kar-ta-kwana a kan yunwa tare da haɗin gwiwar wasu kungiyoyin agaji da nufin shawo kan rashin abinci arewacin Nijeriya.
Mai magana da yawun sa Stephane Dujarric ta tabbatar da haka, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a helkwatar majalisar da ke birnin New York.
Ta ce jami’an su a Nijeriya sun sanar da su irin matsanancin halin da ake ciki, musamman a yankin arewa, don haka kafa kwamitin ya zama dole.
Majalisar Dinkin duniya, ta ce shirin zai taimaka a fanin abinci da lafiya da bada kariya da samar da ruwan sha mai tsafta da kuma inganta tsafta, wanda zai bukaci dala miliyan 250 domin kai wa ga mutanen da su ka fi shiga matsananci hali sakamakon rashin abinci.
You must log in to post a comment.