Home Labaru Rikicin Jam’iyyar PDP: Uche Secondus Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Rikicin Jam’iyyar PDP: Uche Secondus Ya Tsallake Rijiya Da Baya

52
0
Secondus- PDF

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus, ya tsallake yunkurin tsige shi daga kujerar shugabancin jam’iyyar da wasu ‘yan kwamitin zartarwa su ka yi.

A ranar Talatar da ta gabata ne, daukacin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP a su ka taru domin dakile wata takaddamar shugabanci da ta yi kokarin farraka jam’iyyar.

Lamarin dai ya kara kamari ne, bayan wasu ‘yan kwamitin zartarwa 6 sun kada kuri’ar kin amincewa da salon shugabancin jam’iyyar a karkashin jagorancin Uche Secondus, inda su ka bukaci ya sauka daga mukamin sa nan take.

Sai dai a wani martani da ya maida, Uche Secondus ya ce masu da’awar da ya kira ‘yan tsiraru ba su da hujjar neman ya sauka daga mukamin sa, domin bai san ya aikata wani laifin da zai sa ya yi hakan ba.

Wannan na zuwa ne, bayan da a makon da ya gabata wasu shugabanni 7 su ka gabatar da takardun su na yin murabus daga mukaman su, bisa zargin Secondus da maida su saniyar ware a lamurran jam’iyyar.