A yau ne Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya shirya tarbar tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Super Eagles a Fadarsa da ke Abuja.
A na kyautata zaton cewa, Tinubu zai yi musu godiya ne game bajintar da su ka nuna wajen samun nasarar kaiwa wasan karshe na kofin kasashen Afirka AFCON 2023 da a ka kammala a kasar Cote de’Voire.
Idan ba a manta ba, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa yan wasan da sauran jagororin tawagar ta Super Eagles a kan rawar da su ka taka a gasar.
Tinubu ya bayyana tawagar a matsayin jajirtattun yan kasa da su ka yi iyakar kokarinsu wajen daukaka sunan Nijeriya a idon duniya a fagen kwallon kafa, ya ku ma bukaci dukkan yan Nijeriya da su yi kokarin kare martaba da sunan Nijeriya a duk inda su ka samu kansu.