Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce gwamnatin shugaba Buhari bata da wani katabus na kawo cigaba a Nijeriya.
Obasanjo ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a akan zagawoyar ranar dimokradiyya.
Idan dai ba a manta ba, an samu sabani tsakanin Obasanjo da shugaba Buhari gabanin zaben shekara ta 2019, wanda hakan ya sa obasanjo ya mara wa Atiku Abubakar baya a takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyya PDP.
A karshe Obasanjo ya ce, duk da nasara da cigaba da Nijeriya ta samun tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a shekara ta 1999, salon da gwamnatin Buhari ta dauka ba zai haifar wa Nijeriya da mai ido ba.
You must log in to post a comment.