Home Labaru Bayan Zabe: Ahmad Lawan Da Omo Agege Sun Kaiwa Buhari Ziyarar Ban...

Bayan Zabe: Ahmad Lawan Da Omo Agege Sun Kaiwa Buhari Ziyarar Ban Godiya

329
0

Sabon zababben shugaban majalisar dattawa sanata Ahmad Lawan da mataimakin sa Omo Agege, sun kaiwa shugaban kasa Muhammdu Buhari ziyarar ban godiya a kan rawar da ya taka wajen nasarar da suka samu.

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin su shugabannin majalisar ne a daran Talatar da ta gabata a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Idan dai ba a manta ba, Sanata Ahmad Lawan ya lashe zaben shugabancin majalisar dattawa ne da kuri’u 79 yayin da abokin takarar sa Ali Ndume ya samu kuri’u 28.

Haka kuma Sanata Omo Agege ya lashe zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa da kuri’u 68 yayin da abokin hamayyar sa Ike Ekweremadu ya samu kuri’u 37.