Home Labaru Adawa: Atiku Ya Soki Lamirin Kaddamar Da 12 Ga Yuni A Matsayin...

Adawa: Atiku Ya Soki Lamirin Kaddamar Da 12 Ga Yuni A Matsayin Ranar Dimokradiyya

331
0

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce ranar 12 ga watan Yuni shi ne ruhin fafutukar dimokradiyya da Nijeriya ta yi kuma shi ne kofa a rayuwar sa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya ce muhimmancin da ke tattare da bikin ranar 12 ga watan Yuni, zaben Shugaban kasa na shekara ta 1993, ya kasance abin tunawa a tarihin Nijeriya  wajen zama kasa mai ‘yanci.

Ya ce shekaru 26 da su ka wuce, ‘yan Nijeriya sun zabi dimokradiyya a kan mulkin soji, kuma ba don su sauya mulkin sojoji zuwa ga mulkin mutum daya ne ba.

A cewar sa, manufar ranar 12 ga watan Yuni ba wai kaddamar da ita a matsayin ranar Dimokradiyya ba ne kawai, ya na mai sukar lamirin hakan da cewa, babu yadda za a ce an kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu alhalin ‘yan Nijeriya na tunanin ta ina abincin su na gobe zai fito.

Leave a Reply