Home Labaru Abin Da Ya Sa ‘Yan Awaren Kamaru Da Na Nijeriya Su Ka...

Abin Da Ya Sa ‘Yan Awaren Kamaru Da Na Nijeriya Su Ka Haɗe Kai

19
0

Bisa ga dukkan alamu, Rikicin ‘an awaren Kamaru na tsawon shekaru biyar ya fara daukar sabon salo, inda rahotanni ke cewa kungiyoyin awaren na bangaren da ke magana da Turancin Ingilishi su na samun taimako daga kungiyar ‘yan awaren Biafra ta Nijeriya.

Bayan hare-hare biyu da ‘yan awaren na Kamaru su ka kai, inda su ka hallaka sojojin Kamaru 15 a watan da ya gabata, hukumomin sojin sun fitar da wata sanarwa, wadda a cikin ta su ka ce ‘yan gwagwarmayar sun yi amfani da manyan makamai, abin da su k ace ya saba wa dokokin duniya.

Hukumomin sun kara da cewa, karin karfin da ‘yan awaren ke samu ya na da alaka da hadin kan da su ke samu daga wasu kungiyoyin ta’addanci da ke aiki a wajen kasar.

Kakakin rundunonin tsaron Kamaru Kanar Cyrille Atonfack Nguemo, ya ce ba a san ko sojojin Kamaru su na zargin wasu kungiyoyi su na taimaka wa ‘yan awaren ba.

Amma kungiyar aware ta Kamaru, ta Ambazonia Defense Forces ta tabbatar da yin hadaka da kungiyar awaren Biafra da ke neman ballewa daga Nijeriya.