Home Labaru Abba Gida-Gida Ya Fara Ɗaukar Matakan Binciken Gwamnatin Ganduje

Abba Gida-Gida Ya Fara Ɗaukar Matakan Binciken Gwamnatin Ganduje

1
0

Sabon gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya fara daukar
matakan binciken tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar
Ganduje, inda tuni ya bada umarni a kan wasu tsauraran
matakai.

Daga cikin matakan da ya fara dauka, gwamnan ya soke duk cinikin da aka yi na saida wasu wurare mallakin gwamnatin jihar Kano.

Da ya ke jawabi bayan ya karbi rantsuwa, gwamnan ya ba hukumomin tsaron jihar umurmin su karbe iko da wuraren da gwamnatin ganduje ta saida.

Wasu daga cikin wuraren da aka saida dai sun hada da filayen makarantu da masallatai da makabarta da sauran su.

Gwamnan ya kara da cewa, duk matakan da zai dauka a ‘yan kwankin da ke tafe zai yi ne da nufin dawo da kima da martabar jihar Kano.