Home Labarai Abba Gida-Gida Na NNPP Ya Ƙaryata Ji-ta-Ji-tar Zai Nemi Gudummawar Kuɗi

Abba Gida-Gida Na NNPP Ya Ƙaryata Ji-ta-Ji-tar Zai Nemi Gudummawar Kuɗi

52
0

Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf Gida-gida, ya ƙaryata ji-ta-ji-tar cewa zai nemi gudummawar karo-karon kuɗin yakin neman zabe a wajen gangamin mabiya ɗariƙar Kwankwasiyya.

Ji-ta-ji-tar da ake watsawa a shafukan sada zumunta dai na cewa, Abba Gida-Gida zai nemi gudummawar naira dubu 1 daga kowane mutum domin ya tara kuɗin yakin neman zaɓen gwamna a shekara ta 2023.

Kakakin Yaɗa Labaran Abba Sanusi Bature, ya ce ƙarya ce da yarfen siyasa don kawai a ɓata kyakkyawan sunan da ɗan takarar ke da shi.

Ya ce Abba Gida-gida bai ƙirƙiro ko tunanin ƙirƙirar wata gidauniyar neman a tara masa kuɗin yakin neman zabe ba.