Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf Gida-gida, ya ƙaryata ji-ta-ji-tar cewa zai nemi gudummawar karo-karon kuɗin yakin neman zabe a wajen gangamin mabiya ɗariƙar Kwankwasiyya.
Ji-ta-ji-tar da ake watsawa a shafukan sada zumunta dai na cewa, Abba Gida-Gida zai nemi gudummawar naira dubu 1 daga kowane mutum domin ya tara kuɗin yakin neman zaɓen gwamna a shekara ta 2023.
Kakakin Yaɗa Labaran Abba Sanusi Bature, ya ce ƙarya ce da yarfen siyasa don kawai a ɓata kyakkyawan sunan da ɗan takarar ke da shi.
Ya ce Abba Gida-gida bai ƙirƙiro ko tunanin ƙirƙirar wata gidauniyar neman a tara masa kuɗin yakin neman zabe ba.














































