Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya buƙaci ‘yan Najeriya su riƙa yin adalci a duk lokacin da su ke sharhi a kan matsalar tsaro, inda ya ce su riƙa kwatantawa da abin da gwamnatin sa ta gada tun a shekara ta 2015.
Buhari ya bayyana haka ne, lokacin da Khalifan Tijjaniyya na duniya ya kai ma shi ziyara, inda ya ce ya kamata jama’a su rika magana a kan nasarorin da su ka samu a ɓangaren tsaro musamman a yankunan arewa maso gabas da kudu maso kudancin Nijeriya.
Shugaba Buhari, ya ce gwamnatin shi na sane da irin haƙƙoƙin da su ka rataya a wuyan ta, wadanda su ka shafi tsaro.
Buhari ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya su bada haɗin kai da kuma nuna goyon baya a harkar tsaro da kuma yaba wa ayyukan da gwamnati ke yi, inda ya ce sun yi bakin ƙoƙarin su kuma za su cigaba da yi ta hanyar samar da tsare-tsare masu kyau domin yaƙi da ta’addanci.
Daga Cikin ‘yan tawagar da ta ziyarci shugaba Buhari dai akwai Gwamna Umar Ganduje na jihar Kano, da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da kuma Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
You must log in to post a comment.