Home Home A Daina Kallon Aikin Soja Wurin Samun Aiki – Babban Hafsan BoJojin...

A Daina Kallon Aikin Soja Wurin Samun Aiki – Babban Hafsan BoJojin Najeriya

88
0
A Daina Kallon Aikin Soja Wurin Samun Aiki - Babban Hafsan Jojin Najeriya

Babban Hafsan Sojojin Nijeriya Faruk Yahaya, ya ce masu hanƙoron shiga aikin soja su sa a ran su cewa za su shiga ne domin kishin ƙasa da sadaukarwa su daina yi wa aikin kallon wani wurin samun kudi.

Janar Faruk Yahaya, ya ce aikin soja aiki ne na kare Nijeriya ba wurin aikin samun kuɗi ba.

Babban Hafsan ya bayyana haka ne, lokacin da ake yi wa masu neman shiga aikin kuratan sojoji gwajin juriyar gudun kilomita 10 a Cibiyar Gwajin Horon Sabbin Suratan Sojoji da ke Dajin Falgore a Jihar Kano.

Bayanin Laftanar Janar Yahaya dai ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar Sojin Nijeriya Onyema Nwachuku ya fitar a Abuja, inda ya ce shiga aikin soja ba kamar samun aiki ba ne a wasu fannoni na rayuwa, aiki ne na sadaukarwa ɗwajen kare Nijeriya.