Home Labarai 2023: Sufeto Janar Ya Gargaɗi ‘Yan Sanda Kada Su Goyi Bayan Wata...

2023: Sufeto Janar Ya Gargaɗi ‘Yan Sanda Kada Su Goyi Bayan Wata Jam’iyya

90
0

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba, ya umarci ɗaukacin ‘yan sandan Nijeriya su tsaya a tsakiya ba tare da nuna goyon baya ga kowace jam’iyya ba a lokutan yakin neman zabe har zuwa kammala zaɓe.

Alkali Baba ya yi gargaɗin ne, lokacin da ya ke jawabi a wajen taron manyan jami’an ‘yan sanda masu muƙamin Kwamishina zuwa sama.

An dai shirya taron ne a Abuja, ƙasa da kwanaki bakwai kafin a fara gangamin yakin zaɓen shugaban ƙasa, wanda za a yi ranar 25 ga watan Fabrairu na shekara ta 2023.

Shugaban ‘yan sandan, ya kuma gargaɗe su da cewa, a kullum su riƙa kasancewa cikin shiri, tare da nuna ƙwarewa da sanin ya kamata, su kuma rika nuna adalci a tsakanin jam’iyyun siyasa.

Ya ce su sani aikin su shi ne kare masu jefa ƙuri’a daga masu aikata duk wasu laifuffuka, sannan su yi aikin su ba tare da nuna bambanci ko son kai ko fifita wasu a kan wasu ba.