Home Labaru 2023: Majalisa Ta Miƙa Wa Buhari Ƙudirin Dokar Zaɓe Da Ta Yi...

2023: Majalisa Ta Miƙa Wa Buhari Ƙudirin Dokar Zaɓe Da Ta Yi Wa Kwaskwarima

443
0

Majalisun Dokoki na tarayya, sun miƙa ƙudirin dokar zaɓe da su ka yi wa kwaskwarima ga Shugaba Buhari domin ya sanya mata hannu.

Mai taimaka wa shugaban kasa a kan harkokin Majalisar Dattawa Sanata Babajide Omoworare ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce miƙa wa shugaban ƙasa ƙudirin ya dace da sashe na 58 (3) na Kundin Tsarin Mulki na shekara ta 1999, ya na mai cewa Akawun Majalisa Olatunde Ojo ne ya aika da kwafin kuɗirin a ranar Litinin da ta gabata.

A watan Disambar da ya gabata ne, shugaba Buhari ya ce ba zai sanya wa dokar hannu ba har sai an gyara sashen da ya tilasta wa jam’iyyun siyasa yin zaɓen ‘yar tinƙe wajen fitar da ‘yan takara.

Tuni dai majalisun sun gyara dokar, tare da ba jam’iyyu zaɓin ‘yar tinƙe ko na wakilai da kuma masalaha, yayin da hukumar zaɓe ta ce abin da take jira kenan kafin ta fitar da jadawalin zaɓen shekara ta 2023.

Leave a Reply