Home Labaru 2023: Aisha Buhari Na So Kowace Jam’iyya Ta Tsaida Mace Takarar Mataimakiya

2023: Aisha Buhari Na So Kowace Jam’iyya Ta Tsaida Mace Takarar Mataimakiya

25
0

Uwargidan Shugaban Ƙasa A’isha Buhari, ta yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasar Nijeriya su tsaida mace a matsayin ‘yar takarar muƙamin Mataimakiyar Shugaban Ƙasa.

A’isha Buhari ta bayyana haka ne, yayin da ta ke jawabi a wajen taron buɗe-baki da ta gayyaci ‘yan takara daga jam’iyyu daban-daban, wanda ya gudana a Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ta ce adalcin da ya kamata a yi wa mata a yanzu shi ne, a ƙara masu damar shiga cikin gwamnati da shugabancin manyan muƙaman siyasa.

A karshe ta yi kira ga duk ‘yan takarar shugaban ƙasa su maida hankali wajen ƙarfafa haɗin kan Nijeriya da ƙarfafa zumunci da kuma kusantar juna.