Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya ce ya samu nasarar kai ga haƙo ɗanyen mai ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas a kowacce rana.
Shugaban Kamfanin Malam Mele Kyari ne ya bayyana hakan yau Alhamis, yayin taron manema labarai da ya gudana a na Abuja.
Ya ce alƙaluman da aka samu sun haɗa daga watan Yuni zuwa Nuwamban da muke ciki.
Kamfanin wanda cikin shekara 15 da suka gabata ya yi ta fama da rashin taron na masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan harkokin kasuwancin masu zuba jari kuma hakan ya ja raguwar yawan gangar man da yake samarwa a kowacce rana.
Mele Kyari, ya ce suna ta fafutukar ganin yadda za su haɓaka yawan man da ake haƙowa domin ci gaban ƙasa da kuma saukakawa al’umma.
Ya ce an taɓa haƙo ganga miliyan biyu da dubu ɗari biyar a sehkarun baya, amma daga nan aka yi ta fama da rashin saka jari da kuma rashin tsaro har ta kai man da ake haƙo wa ya yi ƙasa zuwa ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu a wannan shekara.
hakan ne ya sa suka tashi da yin aiki tukuru domin samo bakin zaren matsalar.