Home Labaru Ɓangaren Gwamna Ganduje Ya Sake Shan Kaye A Kotu

Ɓangaren Gwamna Ganduje Ya Sake Shan Kaye A Kotu

544
0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da bukatar da ɓangaren Gwamna Ganduje na jihar Kano ya gabatar cewa ta jingine hukuncin da ya tabbatar da zaben shugabannin jam’iyyar APC da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya gudanar.

Kotun, a ƙarƙashin Mai Shari’a Hamza Mu’azu, ta ƙi amincewa da bukatar da bangaren Ganduje ya gabatar saboda ba baya da hurumin gabatar da irin wannan bukata, kasancewar ya daukaka kara a wata kotu.

Haka kuma, Kotun ta tabbatar da hukuncin da ta yi cewa zaben da ɓangaren Shekarau ya yi na shugabannin jam’iyyar APC ya na nan daram, kuma su na da ‘yancin zaben shugabannin jam’iyyar na jiha.

Daya daga cikin Lauyoyin da ke tsaya wa bangaren Ganduje Barista Duru Marcel, ya ce a irin tasu fahimtar hukuncin ya yi musu dadi domin abin da doka ta tanada kenan.

Ya ce Kotun ba ta da hurumin sauraren bukatar da su ka gabatar, kasancewar sun daukaka kara game da hukuncin da ta yanke tun da farko.

LEAVE A REPLY