Home Home  ‘Ƴan Sanda Sun Tsare Basaraken Da Ya Yi Lalata Da Yaro Ɗan...

 ‘Ƴan Sanda Sun Tsare Basaraken Da Ya Yi Lalata Da Yaro Ɗan Shekara 14 A Zaria

46
0
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ta kama wani basarake a birnin Zariya bisa zargin ya yi wa yaro dan shekaru 14 fyade.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ta kama wani basarake a birnin Zariya bisa zargin ya yi wa yaro dan shekaru 14 fyade.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna Muhammadu Jalige ya sanar da haka, inda ya ce rundunar za ta maka basaraken kotu da zarar sun kammala bincike.

Da ya ke tattaunawa da manema labarai, wani ɗan’uwan yaron mai suna Hamza Zubairu, ya ce basaraken ya yi lalata da kanen sa ne a unguwar Kwarbai, wanda a cewar sa, basaraken makwafcin su ne kuma kowa ya na yi ma shi kallon dattijon arziki.

Jami’ar cibiyar kula da wadanda aka yi wa fyade da ke babban asibitin Gambo Sawaba a Zariya A’isha Ahmed, ta ce cibiyar ta gudanar da gwaje-gwaje, kuma za ta mika wa ‘yan sanda sakamakon gwajin nan ba da daɗewa ba.