Home Labaru ‘Ƴan Bindiga Sun Tafka Ɓarna a Birnin Gwari

‘Ƴan Bindiga Sun Tafka Ɓarna a Birnin Gwari

27
0

Al’ummar ƙauyen Damari da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, yanzu haka su na ƙoƙarin tantance ɓarnar da ‘yan bindiga su ka tafka a wani hari da su ka kai ranarAlhamis da ta gabata da daddare.

Barnar ‘yan bindigar dai ta yi sanadiyyar kashe mutane biyar tare da sace wasu, waɗanda har yanzu ba a tantance yawan su ba.

Shugaban ƙungiyar ci-gaban masarautar Birnin Gwari Ishak Usman Kasai ya tabbatar wa manema labarai cewa, ɓarayin sun shiga ƙauyen ne a wani lamari mai kama da ramuwar gayya, bayan artabun da su ka yi da wasu mahara da ake zargin ‘yan ƙungiyar Ansaru ne.