Home Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ƴan Sanda 10 A Jihar Kogi

Ƴan Bindiga Sun Sace Ƴan Sanda 10 A Jihar Kogi

140
0

‘Yan bindiga sun sace jami’an ‘yan sanda da ke karkashin jihar Nasarawa a jihar Kogi a ranar Lahadin da ta gabata.

‘Yan sandan sun faɗa tarkon ‘yan bindigar ne a hanyar dawowa daga jihar Osun, bayan kammala zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.

Wata majiya ta ce, an tura ‘yan sandan zuwa jihar Osun ne domin tabbatar da an yi zaɓen gwamnan jihar lafiya.

Majiyar ta cigaba da cewa, an yi garkuwa da jami’an ‘yan sandan ne a garin Obajana da ke jihar Kogi, inda bayan jami’an da aka tura wurin sun isa, sai su ka iske wata mota kirar Bus mai ɗaukar fasinjoji 18 da wani direba a ciki mai suna Usman Abdullahi da wasu mutane 6 a ciki.

Mutanen sun bayyana wa ‘yan sandan cewa, motar su ce ta lalace sai su ka tsaya su gyara, su na cikin haka ne kwatsam sai su ka ji an afka masu da bindigogi aka sace ‘yan sanda 10.