Home Labarai Barazanar Sanatoci: Shugaban Kasa Buhari Ya Kira Taron Majalisar Tsaro

Barazanar Sanatoci: Shugaban Kasa Buhari Ya Kira Taron Majalisar Tsaro

34
0


Sa’o’i kadan bayan da Sanatoci suka yi barazanar tsige shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari idan har matsalar tsaro ba ta gyaru ba, shugaban ya kira taron gaggawa na majalisar tsaron kasa.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Philip Aduda, wanda ya jagoranci zanga-zangar bayan da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ki amincewa da wani yunkuri na muhawara a kan kalubalen tsaro da aka fuskanta a baya-bayan nan, ya ce ‘yan majalisar sun amince da wa’adin makonni shida ga shugaban kasa domin ya magance tabarbarewar tsaro a halin yanzu, ko a tsige shi.

Sai dai ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, wanda ya yi magana kan barazanar ‘yan majalisar a lokacin da yake amsa tambayoyi ga manema labarai, bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya a fadar shugaban kasar, ya ce shugaban na dukkan mai yiwu wa wajen magance matsalar da ta ki ci taki cinyewa.

Rahotanni daga kasar na cewa ‘yan majalisar sun yanke shawarar ba shugaban kasa wa’adin makonni shida a wani zama na sirri, ko dai a kawo karshen matsalar tsaro, ko kuma su dauki matakin tsige shi.