Home Home Ƙazamin Yaƙin 2023: APC Ta Ce Atiku Ba Shi Da Nagartar Da...

Ƙazamin Yaƙin 2023: APC Ta Ce Atiku Ba Shi Da Nagartar Da Zai Iya Riƙe Amanar Najeriya

79
0
Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu na jam’iyyar APC, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ba abin ba amanar riƙon Nijeriya ba ne.

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu na jam’iyyar APC, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ba abin ba amanar riƙon Nijeriya ba ne.

Kakakin kwamitin Bayo Onanuga ya bayyana haka, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce kamata ya yi hukumar NDLEA ta kama Atiku Abubakar, ta bincike shi dangane da zargin harka da miyagun ƙwayoyi da aka yi masa a cikin wani faifan murya da aka watsa.

Onanuga, ya yi kira ga hukumar EFCC ta gayyaci Atiku Abubakar dangane da zargin harƙallar maƙudan kuɗaɗe da wani mai suna Micheal Achimugu ya yi masa.