Home Labaru Kasuwanci Ƙarin Kuɗin Wutar Lantarki: NLC Ta Zargi Gwamnati Da Rashin Tausayi

Ƙarin Kuɗin Wutar Lantarki: NLC Ta Zargi Gwamnati Da Rashin Tausayi

53
0

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da waɗansu kungiyoyin fararen hula sun yi tir da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da tsarin wuta mai daraja ta ɗaya wato Band A.

A zantawa da wasu daga cikin ’yan rajin kawo canji da kuma ’ya’yan kungiyar NLC, sun ce duk dalilan da jami’an gwamnati suka bayar kan karin kudin ba hujjoji ba ne.

A cewar su, ko a ƙasashen da aka ci gaba, ana tallafa wa wasu ɓangarori kamar na man fetur da wutar lantarki.

A jiya Laraba ce dai hukumar kula da wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar da ƙarin kuɗin kilowatt na wuta daga Naira 68 zuwa Naira 225.

Wannan karin ga masu amfani  da tsarin Band A da ke samu wuta na tsawon sa’o’i 20 a kullum za su riƙa biyan Naira 135,000 kowane wata.

A taron da mataimakin shugaban NERC, Musiliu Oseni ya yi da manema labarai a Abuja, ya ce karin zai shafi kaso 15 na masu amfani da wutar lantarki miliyan 12 ne a Najeriya.

Shugaban yada labarai a hedikwatar NLC, Benson Upah kuwa, ya ce Ƙungiyar ta su za ta ɗauki matsaya kan mummunan ta’asar da aka yi na ƙarin kuɗin wutan.

Leave a Reply