Sojojin Isra’ila sun ce sun shirya kai Falasɗinawan da suka rasa muhallan su a Gaza zuwa abin da suka kira cibiyoyin jin-ƙai a tsakiyar zirin gabanin ƙaddamar da ƙudurin su na kai hari ta ƙasa.
Sun ce za su kwashe mutanen ne daga Rafah a kudancin Gaza zuwa tsibiran sannan kuma za su ba su kayan jin ƙai da kuma muhalli na wucen gadi duk da wurin da ake shawarar kai su ya lalace sakamakon yawan hare-haren da aka kai ta sama da ƙasa.
Rafah dai ta cunkushe da fiye da Falasɗinawa miliyan ɗaya waɗanda hare-haren Isra’ila suka tilasta masu tserewa daga gidajensu a Gaza.
Duk da gargaɗin da ƙasashen duniya suka yi, Isra’ila ta dage cewa kai hari ta ƙasa kan birnin ne hanya tilo ta murƙushe Hamas.
Amurka ta ce dole ne Isra’ila ta nuna tana da wani tsari na kare farar hula kafin kai irin wannan hari a Rafah.