Home Home Zulum Ya Bada Umarnin Binciken Ma’aikatan Asibitin Da Suka Ƙi Karɓar Waɗanda...

Zulum Ya Bada Umarnin Binciken Ma’aikatan Asibitin Da Suka Ƙi Karɓar Waɗanda Suka Yi Haɗari

205
0

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya umurci ma’aikatar lafiya ta yi bincike tare da kamo ma’aikatan lafiya da ke bakin aiki bisa zargin ƙin amincewa da waɗanda hatsari ya rutsa da su a asibitin Umaru Shehu da ke Maiduguri.

Ziyarar da gwamnan ya kai asibitin dai, ta na zuwa ne a matsayin martani ga wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, wanda ke nuna yadda wasu jami’an kiwon lafiya su ka ƙi amincewa da waɗanda hatsarin ya rutsa da su.

 Gwamnan Zulum dai ya bada wa’adin sa’o’i 24 ga ƙungiyar bincike domin gano ma’aikatan kiwon lafiyar da abin ya shafa da kuma bada shawarwarin da su ka dace.

Ya ce abin da ya faru rashin mutunci ne kuma ba abin yarda ba, musamman yanayin da aka bar marasa lafiya su na kuka don neman taimako, amma asibiti ta ƙi karɓar su, don haka babu dalilin da zai sa ba za a ɗauki matakin ladabtarwa a kan ma’aikatan da su ka yi kuskure a asibitin ba.

Leave a Reply