Home Labarai Ziyara: Shugaba Tinubu Zai Tafi Faransa

Ziyara: Shugaba Tinubu Zai Tafi Faransa

39
0
download 2024 06 13T122639.568
download 2024 06 13T122639.568

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu zai yi tafiya zuwa ƙasar Faransa a yau Litinin, kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana.

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Sai dai ba a fayyace makasudin ziyarar ba, amma ana sa ran shuagab Tinubu zai dawo gida Najeriya bayan wani dan lokaci kadan.

Wannan ziyarar ta biyo bayan ziyarar da ya kai kasar Equatorial Guinea a baya-bayan nan, inda ya gana da shugaban ƙasar Teodoro Mbasogo, suka yi shawarwari,

da kuma sanya hannu kan yarjejeniyar man fetur da iskar gas, da kuma tsaro.

Leave a Reply