An Fara Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro A Nijeriya.
Nijeriya ce kasar dake da kashi 27 cikin 100 na masu dauke da cutar zazzabin cizon sauro a duniya.
Sannna kasar nan na da kuma kashi 31 na wadanda cutar ke kashewa a duniya, kamar yadda rahoton malaria na duniya na 2023 ya nuna.
Akalla mutum 200,000 ne suka rasu a sanadiyar cutar zazzabin cizon sauro a shekarar da ta wuce.
Kazalika, yara ‘yan kasa da shekara biyar da mata masu ciki ne suka fi saurin kamuwa.
Nijeriya ta karbi allurar rigakafin cutar a watan Oktoba, sannan an fara allurar a jihohin Bayelsa da Kebbi.
Daga bisani za a fadada rigakafin zuwa wasu jihohin nan da wasu watanni masu zuwa.