Malaman Makarantar Firamare a Babban Birnin Tarayya, sun fara sabon yajin aiki, wanda hakan ya hana ɗalibai kammala jarabawar zangon karatu na farko da suka fara.
Yajin aikin na nuna rashin gamsuwar malaman kan gazawar shugabannin ƙananan hukumomi na aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da biyan bashin da suke bi.
Wannan shi ne karo na biyu da malaman ke tsunduma yajin aiki a wannan zangon karatun.
Wannan na zuwa ne bayan yajin aikin farko da suka yi a watan Satumba.
Ɗaliban da suka tafi makaranta domin rubuta jarabawa, an kora su gida.
Da yake magana kan batun, Shugaban Ƙungiyar Malamai ta NUT reshen Kubwa, Kwamared Ameh Baba, ya ce, an gaza cika musu alƙawarin da aka ɗaukar musu.
Inda ya kara da cewa Shugabannin ƙananan hukumomi sun gaza biyan sabon mafi ƙarancin albashi da aka amince da shi kuma har yanzu muna binsu bashin albashi.
Kwamared Baba, ya tabbatar da cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi tare da alƙawarin biyansu albashin watan Nuwamba.














































