Home Labarai Zargin Ta’addanci: Shugaban Karamar Hukumar Yagba da ‘Yan Banga na Neman Hallaka...

Zargin Ta’addanci: Shugaban Karamar Hukumar Yagba da ‘Yan Banga na Neman Hallaka ni – Ardo Babuga

79
0
OIP (2)
OIP (2)

Ardon masarautar Yagba ta yamma dake Jihar Kogi Ardo Babuga Mairali, ya koka game da yadda shugaban karamar hukumar  Yagba ta yamma, Hon. Tosin Olokun yake neman hallaka shi ta hanyar yin amfani da yan kungiyar sa kai ta banga wajen ci masa mutunci.

Ardo Babuga ya ce duk da cewa tsohon gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda, ya shiga maganar har ta kai  ga ya hada shi da gwamnan Jihar Kogi, inda  suka zauna suka tattauna Kuma kai tsaye gwamnan ya kira shugaban karamar hukumar ta Yagba, amma ya sake cinno masa Jami’an yan banga lamarin da ya kaiga yanzu haka an wawushe masa duk abinda ya mallaka.

Haka kuma, Ardo Babuga Mairali,  ya koka bisa yadda ya kashe makudan kudade ciki har da yin belin kansa daga hannun Jami’an tsaro akan naira miliyan biyar mamma har yanzun ana farautar kamar  ake ake farautar zumo.

Ya kuma zargi maitaikawa gwamna kan harkokin tsaro Commodore Omodoro Duru Jerry da hada baki da shugaban karamar hukumar domin gallaza masa.

Duk kokarin da manema labarai suka yi domin jin ta bakin wadanda ake zargi, amma lamarin ya gagara saboda wayoyinsu a kasha.

Karshe dai ya na neman tallafin alummar yan Najeriya kan wannan matsalar da yake ciki.

Leave a Reply