Gwamnan Jihar Neja Muhammad Umar Bago, ya bada
tabbacin fara aikin gyaran hanyar Kontagora zuwa Tagina da
kuma Minna.
Umar Bago ya bada tabbacin ne, lokacin da ya kai wa Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Muhammad Barau Mu’azu II, ziyarar Sallah a masarautar Kontagora.
Ya ce hanyar Kontagora zuwa Tagina, da kuma Tagina zuwa Minna ta na buƙatar kulawa matuƙa, domin a ba jama’a damar zirga-zirga cikin aminci da kuma kiyaye aukuwar haɗurra.
Hanyoyin da lamarin ya shafa dai hanyoyi ne masu muhimmanci, wadanda sun daɗe da lalacewa, amma ba su samu kulawar gwamnatin baya ba.
Gwamnan ya kuma jaddada cewa, zai cika ɗaukacin alƙawurran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe, wadanda su ka haɗa da gyara madatsun ruwa domin magance matsalolin ambaliya da wasu yankunan arewacin jihar ke fuskanta.














































