Hukumar kula da dokokin fannin albarkatun man fetur da
iskar gas ta Nijeriya, ta bayyana wa dillalan man fetur cewa
kofar ta a bude ta ke ga duk wanda ke bukatar samun lasisin
shigo da man fetur muddin zai bi ka’idodin da doka ta tanada.
Shugaban hukumar Injiniya Faruk Ahmed ya bayyana haka, jim kadan bayan ganawa da dillalan man fetur a Abuja, inda ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su bi ka’idojin neman lasisi domin shigo da mai kamar yadda doka ta tanada, sannan ya ja kunnen dillalan su guji cutar da ‘yan kasa ta hanyar sanya farashi fiye da yadda ya kamata.
Masani a fannin albarkatun man fetur a Nijeriya Malam Yabagi Sani, ya ce matakin da hukumar ta dauka ya zo daidai da akidar tafiyar da tattalin arzikin kasa, wanda ya dogara ga tsarin kasuwanci na kasa.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban kungiyar dillalan man fetur masu zaman kan su ta Nijeriya IPMAN, Abubakar Maigandi Dakingari, ya ce muddin aka cika alkawarin bada lasisi kamar yadda aka fada, to su ma dillalan man fetur masu zaman kan su za su iya shigo da man, amma damuwar su ita ce har yanzu kamfanin kasuwancin man fetur na NNPC ya rike masu kudi ba tare da ba su kaya ba tsawon watanni 8.














































