Wata kotu a Jihar Edo ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar a gidan yarin Benin.
Tun daga farko hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa wato EFCC ce ta kai mutanen ƙara bisa zarginsu da amfani da intanet wurin aikata zamba cikin aminci.
Waɗanda aka aika gidan yarin sun haɗa da Amogie Julius da Omogbon Friday Harry da Osaze Okoro da Lucky Tegiri da kuma Omokhua Destiny.
Duka waɗanda ake zargin sun amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa inda cikin laifukan har da batun yin sojan gona ga jam’ian ƙasashen waje da zummar yin zamba ga jama’a don karɓar musu kuɗaɗen su.
You must log in to post a comment.