Home Labaru Zaman Lafiya: Fafaroma Francis Ya Fara Ziyara A Kasashen Afrika

Zaman Lafiya: Fafaroma Francis Ya Fara Ziyara A Kasashen Afrika

359
0

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis da ya fara cikakkiyar ziyara a kasashen Afrika, ya jinjina wa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin gwamnatin Mozambique da ‘yan tawayen kasar, yayinda ya nuna goyon bayansa ga mutanen da ibtila’in guguwa ta shafa a kasar.

Ziyarar na zuwa ne bayan gwamnatin kasar ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da tsohuwar kungiyar ‘yan tawayen Renamo wadda ta rikide ta koma babbar jam’iyyar adawa a kasar.

Yakin basasar tsawon shekaru 16 ya dai-dai-ta Mozambique wadda kasar Portugal ta yi wa mulkin mallaka.

A yayin ganawa da shugaban kasar Filipe Nyusi, Fafaroma Francis ya jaddada godiyarsa ta kashin kansa kan kokarin da aka yi na samar da zaman lafiya a kasar, yana mai cewa, ta hanyar sasantawa ce kawai za a iya shawo kan duk wani kalubale.

Shugaban jam’iyyar Renamo, Ossufo Momade da sauran shugabannin jam’iyyun adawa na cikin mahalarta ganawar da Fafaroman ya yi da shugaban kasar ta Mozambique.

Ziyarar Fafaroman na zuwa ne bayan Mozambique ta fuskanci ibtila’in guguwar Idai da Kenneth, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 600 tare da jefa dubban jama’a cikin halin kuncin rayuwa.

Leave a Reply