Home Labaru Zakzaky Da Mai Dakinsa Sun Koma Najeriya

Zakzaky Da Mai Dakinsa Sun Koma Najeriya

239
0

Shugaban kungiyar Islamic Movement In Najeriya, Sheihk Ibrahim El-Zakzaky da mai dakinsa Zeenatu Ibrahim sun dawo Najeriya daga kasar India, sakamakon rashin gamsuwa da matakan kula da lafiyar su.

Rahotanni sun tabbatar da cewa El-Zakzaky tare da mai dakin sa na hannun jami’an hukumar tsaro ta DSS bayan sun iso Najeriya.

Wani hoton bidiyo da ofishin sa ya wallafa a shafin Twitter, ya nuna malamin na bayani kan musabbin dawowarsa Najeriya, biyo bayan rashin jituwa tsakaninsa da likitocin da za su duba lafiyarsa da ta mai dakinsa a asibitin Medenta na India.

Shugaban kwamitin fafutukar ganin gwamnati ta saki El-zakzaky, Abdullahi Musa, ya ce an hana shi ganawa da likitocin da suka saba duba lafiyar sa a Najeriya, wadanda kuma ke da cikakkiyar masaniya kan Lalurar sa.

Shi ma mai Magana da yawun kungiyar a Najeriya Ibrahim Musa, ya zargi gwamnatin tarayya da katsalandan kan shirin duba lafiyar jagoran su, wanda hakan ya tilasta masa zabin dawowa gida. Sai dai gwamnatin tarayya ta musanta zargin, inda ta ce Ibrahim El-Zakzaky ne ya yi yunkurin karya sharuddan da aka gindaya masa, ta hanyar gabatar da wasu bukatu da suka hada, ajiye shi a babban Otal  dake birnin New Delhi, kuma kada a yi masa shamakin ganawa da dukkanin bakin da suka nemi ziyartar sa.