Home Home Zaben Shugaban Kasa: ‘Yan Slovenia Na Kada Kuri’a

Zaben Shugaban Kasa: ‘Yan Slovenia Na Kada Kuri’a

28
0

Al’ummar Slovenia na kaɗa ƙuri’ar zaɓen shugaban ƙasa, wanda ake fatan ganin mace ta farko ta yi nasara a zaɓen.

Ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna ‘yar takara Natasia Pirc Musar, wadda ‘yar jarida ce kuma lauya, ka iya yin nasara.

Ms Pirc Musar ce kadai ta tsaya takara karkashin jam’iyya mai mulkin ƙasar.

Abokin hamayyar ta Anze Logar kuma tsohon ministan harkokin waje karkashin jam’iyyar Democrats, ya samu kuri’u masu yawa a zagayen farko da aka yi a watan jiya.