Shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce kayen da jam’iyyar ta sha a zaɓen gwamnan jihar Osun jarrabawa ce daga Allah.
Azantawarsa da BBC, Adamu ya ce wajibi ne ‘ya’yan jam’iyyar su gyara abubuwan da ba daidai ba game da tafiyar da siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2023.
Ya ce “Wannan ya nuna cewa akwai aiki a gabansu, inda zasu sauya salon yadda suke gudanar da harkokin jam’iyar.”
Sai dai shugaban jam’iyyar APCn ya ce rashin Nasarar baya nufin jam’iyyar za ta faɗi a babban zaɓen 2023 ba.
A cewarsa jam’iyyar za ta yi nazarin abubuwan da suka sanya jam’iyyar ta faɗi zaɓen na jihar Osun domin ta samu nasara a zaɓen ƙasa mai zuwa.
Ya kara da cewa tabbas akwai rashin jituwa tsakanin ‘yan APC wanda hakan ne ma yasa jiga-jigan jam’iyyar jihar ta Osun suka riƙa suka da zargin junansu.
A cikin wannan wata na Yuni ne Senata Ademola Adeleke na jamiyyar PDP ya samu nasara a kan gwamna Mai ci Gboyega Oyetola na APC, wanda ya nemi wa
adi na biyu, da ratar ƙuri`a kusan dubu talatin.