Home Labaru Zaben Gwamnan Kogi: PDP Ta Gargadi Hukumar INEC

Zaben Gwamnan Kogi: PDP Ta Gargadi Hukumar INEC

353
0

Jam’iyyar PDP ta gargadi hukumar zabe mai zaman kanta INEC kada ta yi yunkurin fakewa da rikici wajen yin magudi a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Kogi.

Kola Ologbondiyan, Babban Sakataren Jam’iyyar Ta Kasa
Kola Ologbondiyan, Babban Sakataren Jam’iyyar Ta Kasa

Babban sakataren Jam’iyyar ta kasa, Kola Ologbondiyan, ya bayyana haka  ga manema labarai a Abuja, ya ce jam’iyyar ta kaddamar da cewa ta na da tabbacin lashe zaben Kogi sannan kuma ya zama dole hukumar INEC ta tabbatar da gudanar da zaben gaskiya, cewa rashin hakan ne ke haifar da wanzuwar rikicin  zabe.

Ya ce ya zama dole hukumar INEC ta isar da gargadi kai tsaye zuwa ga gwamnan jihar Yahaya Bello da jam’iyyar APC domin su janye daga kowani irin rikici a zaben, saboda a shirye mutanen Kogi suke su tunkari gwamnan da jam’iyyarsa gaba-da-gaba. Jam’iyyar ta tunatar da INEC da Yahaya Bello su lura cewa mutane za su yi gangami ne a zaben ranar 16 ga watan Nuwamba, domin juya baya ga gwamnatin rashin adalci.