Home Labaru Zababbun Sanatocin APC 2 Su Na Rububi A Kan Kuri’un ‘Yan PDP...

Zababbun Sanatocin APC 2 Su Na Rububi A Kan Kuri’un ‘Yan PDP A Majalisar Dattawa

98
0

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da Godswill
Akpabio, sun fara kokarin ganin yadda za su samu kuri’un
Sanatocin jam’iyyar PDP.

‘Yan siyasar biyu dai su na daga cikin zababbun ‘yan majalisar dattawan da za a rantsar a jam’iyyar APC, kuma da alama Abdul-Aziz Yari bai hakura da takarar sa ta neman kujerar shugabancin majalisar ba duk kuwa da cewa baya daga cikin manyan Sanatoci.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, Abdul-Aziz Yari ya na bakin kokarin sa domin ganin ya samu goyon bayan zababbun Sanatocin jam’iyyar PDP.

Tuni dai wasu gungun Sanatoci daga jihohin Arewacin Nijeriya su na goyon bayan Abdul-Aziz Yari don ya zama shugaban majalisar Dattawa.

Leave a Reply