Home Labaru Za’A Dauki ‘Yan Banga Domin Gadin Makarantu A Yankin Abuja

Za’A Dauki ‘Yan Banga Domin Gadin Makarantu A Yankin Abuja

52
0

Hukumomin birnin Tarayya Abuja sun ce zasu ɗauki ‘yan banga domin gadin makarantu saboda barazanar tsaron da ake fuskanta.

Jaridar The Punch ta ambato daraktan gudanarwa a ɓangaren tsaro na hukumar birnin na tarayya na cewa an riga an kammala shirin ɗaukar ƴan banga da za su tabbatar da tsaro a makarantu a yankin na Abuja.

Wannan na zuwa ne biyo bayan wasu Rahotannin tsaro da ke cewa ƴan bindiga daga jihohin da ke makwabtaka da Abuja na tsallakowa yankin.

Ƴan bindiga sun sha kai hare-hare makarantu suna satar ɗalibai a yankin arewa maso gabashi, kuma ana ganin satar mutane ta dawo a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A makon da ya gabata gwamnatin Neja da ke makwabtaka da Abuja ta yi gargaɗin cewa mayaƙan Boko Haram sun mamaye wasu yankuna na jihar.