Kungiyar Matasan Arewa AYCF, ta ce za ta nemi diyyar rayukan ‘yan Arewa da aka kashe tare da lalata dukiyoyin su a yankin Kudu maso Gabas muddin aka saki jagoran ‘yan awaren Biafra Nnamdi Kanu.
Shugaban kungiyar Yerima Shettima ya bayyana haka, inda ya ce sakin Nnamdi Kanu zai nuna rauni daga bangaren gwamnati, kuma sakin shi za a iya fassara shi da cewa gwamnati ta na tsoron sa, kuma jami’an tsaro ba su da katabus.
Yerima Shettima ya kara da cewa, kamata ya yi a yi amfani da shari’ar Nnamdi Kanu a matsayin wata aya domin guje wa laifuffukan da za su faru nan gaba.
Ya ce dole ne doka ta dauki matakin da ya dace, yayin da su ka aikata ta’addanci a kan ‘yan Nijeriyan da ba su ji ba ba su gani ba ciki har da mutanen su.
Shetima Yerima, ya ce idan gwamnati ko kotu su ka yanke hukuncin cewa za su saki Nnamdi Kanu, to su sani cewa za su bukaci a biya diyya ga rayukan ‘yan Arewa da miyagun su ka kashe.